Hukumar gudanarwa ta Jami’an Al-Azhar ta kasar Masar ta bada sanarwan korar dalibanta maza
76
daga Jami’ar sanadiyyar karya dokokin jami’ar ta hanyar maida jami’ar dandalin gwagwarmaya da sabbin shuwagabannin kasar wadanda suka kauda mohammad Mursi daga kujerar shugabancin kasar ta Masar.
Tashar Television na Presstv mai watsa shirye shiryen sa da harshen turanci a nan Tehran ya ce, jami’an har’ila yau ta kori dalibai mata a reshenta na Nail Delta su 36 daga Jami’an da laifi iri daya.
Jami’ar Al-Azhar ta kara da cewa ta dau wannan matakin ne bayan ta gudanar da bincike mai zurfi a cikin daliban jami’an ta kuma tabbatar da abubuwan da take zargin daliban da shi.
Tun bayan kifar da gwamnatin Mursi a cikin yulin shekarar da ta gabata dai sabuwar gwamantin kasar ta kashe mutanen fiye da 1400 sannan kotunan kasar ta yanke hukunci kisa da kuma dauri kan daruruwan magoya bayan kungiyar Ikhwanul Muslimin, daga ciki har da shugaban kungiyar.ABNA.